OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Hukumar EFCC Ta Kama Masu Buga Kudin Jabu

Hukumar EFCC Ta Kama Masu Buga Kudin Jabu

 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kasa, EFCC ta ce ta kai wani sumame da kama wasu mutane da suka kware wajen bugawa da siyar da dala ga al’umma.

Mai Magana da yawun hukumar, Wilson Uwajaren ne ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce sumamen na hadin gwiwa ne da hukumar yaki, sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA.

Ya ce sun samu nasarar kama mutane hudu ciki har da wata mata a otal din swiss pearl continental dake layin Koforidua dake Wuse Zone 2 a Abuja.

Ya kara da cewa sun samu kudin jabu har dalal amurka dubu dari hudu da ashirin da bakwai, da dari hudu.

Uwajaren kara da cewa wadanda aka kama sun bayar da bayanai da suka taimaka wajen gano shugaban su, Douglas Mbonu. Ya hori al’umma dasu daina siyan siyan kudaden ketare a gari barkatai domin gujewa fadawa hannun bata gari.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci