OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Hukumar EFCC Na Binciken Faifan Muryar Da Ke Zargin Malami Da Katsalandan A Ayyukan Ta

Hukumar EFCC Na Binciken Faifan Muryar Da Ke Zargin Malami D

Hukumar EFCC

Hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, (EFCC) ta ce ta na bincike kan faifan murya da ke ci gaba da yaduwa wanda ke nuni da babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami na yin katsalandan cikin laifukan cin hanci da hukumar ke aiki a kai.

Bayanin haka na kunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun kakakin ta, Wilson Uwajaren inda ta bayyana wanda ya yi wannan a matsayin dan uwan ​​wani da ake zargi da aikata laifi,  mai suna Mohammed Idris.

Hukumar ta bayyana Idris a matsayin lauya kuma dan sanda dake yi wa hukumar aiki.

An dai jiyo Idris na ikirarin cewa yanzu Malami ne ke rike da hukumar EFCC. Hukumar tana hannunsa. Da zarar Malami ya yi magana, za a bude asusun ajiyar da aka rufe.

Haka kuma Idris ya shawarci wanda yake Magana da shi ta wayar tarho da ya sauya lauyan da ya tsaya masa, sai dai mai maganar ya ce hakan da kamar wuya tunda  Malami ne ya hada su da lauyan.

Ta cikin martanin da EFCC ta yi dai ta ce babu gaskiya cikin ikirarin da Idris din ya yi, kuma tana ci gaba da bincike kan batun, tana mai siffanta  jami’in da mai karbar cin hanci da rashawa ba tare da darajanta dokokin hukumar ba.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci