OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

Hukumar Civil Defence ta kama mutum 7 da suka cire, Suka sayar da shingayen Titi a Imo

Hukumar Civil Defence ta kama mutum 7 da suka cire, Suka say

Photo Source: Jobadung

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da cirewa da sayar da shingayen tituna a jihar Imo.

Kwamandan rundunar na jihar Imo, Chukwuemeka Odimba ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin.

Odimba ya bayyana cewa biyu daga cikin wadanda ake zargin sun cire shingayen tare da sayar wa sauran mutane biyar din.

Ya kara da cewa kama su ya biyo bayan rahoton sirri ne da ya bankado maboyar su.

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan ayyukan barayi a jihar.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su nisanci aikin lalata kadarorin gwamnati.

Ya kara da cewa, rundunar ba za ta nade hannunta ga ayyukan masu barna ba tare da jaddada aniyar sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ba su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai