OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hatsarin Tirela Ya Yi Sanadiyar Rasa Rayuka 9, Da jikkata Mutum 11 A Gombe

Hatsarin Tirela Ya Yi Sanadiyar Rasa Rayuka 9, Da jikkata Mu

A kalla mutane tara ne suka rasa rayukansu yayin da goma sha daya suka tsira da raunuka a wani hatsarin tirela da ya rutsa da su a daren Laraba a Gombe.

AllNews ta tattaro a wurin da hatsarin ya afku cewa tirelar na dauke da jarakuna ne na man gyada. 

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, sashin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Gombe ya bayyana cewa mutane tara ne suka mutu yayin da 11 suka samu raunuka daban-daban.

Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar Gombe, Felix Theman ya tabbatar da cewa hatsarin ya afku ne a mahadar Bomala da ke kan Bye-pass na kudancin jihar da misalin karfe 8 na dare.

Ya bayyana cewa adadin mutanen da hatsarin ya rutsa da su ya kai 20.

 Sai dai an garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa asibitin kwararru na Gombe da kuma asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya Gombe domin samun kulawar da ta dace.

Yayin da yake lura da cewa ba'a amince direba ya wuce iyakar gudun kilomita 40 a cikin sa’a guda a cikin babban birnin ba, Kwamandan ya gargadi direbobi da su guji gudun da ya wuce gona da iri.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci