Mutane 25 sun rasu yayin da 53 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a Gadar sama ta Dangwauro a titin Kano zuwa Zaria.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Kano, Ibrahim Abdullahi ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya fitar ga manema labarai a safiyar yau Litinin.
Abdullahi ya ce hatsarin ya faru ne da babbar motar Tirela IVECo mai lambar XA 311 ZB.
“Mun samu kira da misalin karfe 3:15 na dare a ranar 1 ga watan Yuli, daga nan muka tura jami’anmu zuwa wurin da lamarin ya faru don aikin ceto da misalin karfe 3:30”, inji shi.
Ya ce lamarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da makare mota tare da kaya wanda hakan ya sa motar ta rasa sarrafuwa.
Sannan ya ce bayan kai wadanda lamarin ya shafa asibiti, likitoci sun tabbatar da mutuwar mutane 25.Idan za a iya tunawa dai a ranar Juma’a ma irin hakan ta faru a karamar hukumar Kura inda masallata 18 suka rasa ransu.
0 Tsokaci