Photo Source: Learn Religions
A gobe Juma'a ne ake sa ran jigilar Alhazai na farko daga babban birnin tarayya Abuja zuwa kasa mai tsarki, Saudiyya.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Daraktan hukumar jin dadin alhazai na babban birnin tarayya Abuja, Malam Muhammad Nasiru Danmallam.
Danmallam ya kuma ba da umarnin cewa mahajjatan da za su kasance a sansanin Hajj Transit Camp, Bassan Jiwa, kusa da filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa sansanin zai shirya alhazan domin jigilarsu zuwa kasa mai tsarki.
Daraktan ya kuma ba da umarnin cewa dukkan alhazan da za a kai su ranar Juma’a su zo ranar Alhamis da karfe 10 na safe domin karbar takardun tafiya.
Ya kara da cewa, za a gudanar da gwajin PCR na wajibi ga maniyyatan kamar yadda hukumomin Saudiyya suka tsayar.
Danmallam ya shawarci alhazai da su duba jadawalin jirginsu a sansanin aikin Hajji na dindindin domin sanin jadawalinsu.
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta dauki matakan da suka dace don ganin alhazai sun bi ka’idojin da aka gindaya.
Ku tuna cewa ana sa ran jigilar maniyyata 2000 daga Abuja zuwa kasa mai tsarki.
0 Tsokaci