OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnonin Arewa Sun Gana Da Tinubu, Sun Tattaunawa Akan Zabin Mataimaki

Gwamnonin Arewa Sun Gana Da Tinubu, Sun Tattaunawa Akan Zabi

Northern Governors Forum

Gwamnonin Arewa na jam’iyyar APC sun gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar Alhamis a Abuja.

Gwamnonin da adadinsu ya kai goma sha daya sun kai ziyara ne domin tattauna batun zaben mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar a zaben 2023.

Ana sa ran dan takarar mataimakin shugaban kasa na Tinubu a karkashin jam’iyyar APC zai fito daga Arewa kasancewar shi (Tinubu) ya fito daga kudancin kasar nan.

A wata hira da ya yi da Trust TV a ranar Laraba kamar yadda AllNews ta tattaro, mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Tinubu, Bayo Onanuga ya ce an bar wa gwamnoni shawarar zaben mataimakin shugaban kasa.

Ya bayyana cewa, "Lokacin da Tinubu ya gana da gwamnonin Jam'iyyar a wurin taron su, ya gaya musu cewa 'za ku zama mutanen da za su zaba min mataimaki'."

Idan ba a manta ba Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da wa’adin mako guda ga dukkan jam’iyyun siyasa su mika sunayen ‘yan takarar su na mataimakin shugaban kasa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci