OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnonin APC Sun Amince Da 'Yan Takarar Yarjejeniya Bayan Ganawa Da Buhari

Gwamnonin APC Sun Amince Da 'Yan Takarar Yarjejeniya Bayan G

Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun goyi bayan matakin da aka dauka na ‘yan takarar yarjejeniya a taron jam’iyyar na kasa da za a gudanar a ranar Asabar.

Gwamnonin sun ce tsarin samar da ’yan takarar yana kan gudana.

Shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan.

Bagudu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar gwamnati jim kadan bayan ganawar sa da shugaban kasa a fadar sa da ke Abuja ranar Laraba.

Ya kuma bayyana cewa kowane gwamna yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayanin mukaman da aka ware na jam’iyyar a matakin shiyya.

A halin da ake ciki shugaban ya bayyana sha'awar sa ga jam'iyyar ta samar da shugabanninta ta hanyar yarjejeniya a cikin watan da ta gabata.

Wadanda suka halarci taron da shugaban kasar sun hada da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da gwamnoni 16 na Kaduna, Borno, Kebbi, Plateau, Kogi, Yobe, Ogun, Ekiti, Gombe, Ebonyi, Imo, Niger, Jigawa, Kwara, Zamfara da kuma Jihar Nasarawa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci