Babban daraktan cibiyar bunkasa kwazon aiki ta kasa, Baffa Babba Ɗan’agundi, ya tabbatarwa ‘yan Nijeriya cewa, cibiyar ta tsara wani shiri da zai samarwa ‘yan Nijeriya miliyan daya aikin yi.
Ɗan’agundi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.Ya ce, cibiyar tuni ta fara aiki kan wannan kuduri kuma za ta tattauna da karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi kan shirin.
A cewarsa, idan har shugaban kasa ya amince da shirin, zai samar da ayyukan yi da kuma samar da makudan kudaden shiga na Naira biliyan uku ga gwamnati duk wata.
Ya kara da cewa, shirin da aka yi wa take da ‘National Productivity Movement’ zai kara wa tattalin arzikin kasa kima da samar da damammaki ga ‘yan kasa.
0 Tsokaci