OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Tarayya Zata Rufe Ɗakunan Gwaje-gwajen Likitoci Marasa Rijista

Gwamnatin Tarayya Zata Rufe Ɗakunan Gwaje-gwajen Likitoci M

Gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin rufe dakunan gwaje-gwajen likitocin da ba a yi wa rajista ba a kasar don tsaftace fannin kiwon lafiya.

Karamin Ministan Lafiya, Joseph Ekumamankama ya bayyana haka yayin da ya bukaci mahukunta da ma’aikatan kungiyar kimiyyar dakin gwaje-gwajen lafiya ta Najeriya da kada su yi kasa a gwiwa wajen gudanar da ayyukansu na doka.

Ya yi wannan bayani ne a lokacin da mambobin ƙungiyar karkashin jagorancin magatakardar, Dokta Tosan Erhabor suka kai masa ziyarar ban girma a hedikwatar ma’aikatar lafiya da ke Abuja.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta fitar a ranar Asabar ta hannun Daraktan yada labarai, Ahmed Chindaya, ministan ya bayyana cewa za a samar da tsare-tsare don tabbatar da gudanar da harkokin ƙungiyar cikin sauki.

“Ministan, wanda ya yaba da ziyarar, ya ba tawagar tabbacin goyon baya da goyon bayan ma’aikatar wajen ganin ta cim ma aiki da ayyukan ƙungiyar, ruwaitowar Jaridar Punch.

“Ya ce za a samar da tsare-tsare da za su taimaka wajen gudanar da ayyukansu, yadda ya kamata domin cimma burin shugaban kasa a fannin kiwon lafiya.

“Duk asibitocin da ke karkashin ma’aikatar lafiya ta tarayya za su kasance farkon asibitocin da za su fara aiwatar da cikakken tanade-tanaden dokar, wanda kuma dakunan gwaje-gwaje a asibitocin jihohi za su biyo baya.  

"Da wannan, in ji ministan, za a rufe dakunan gwaje-gwajen likitocin da ba su yi rajista da babbar ƙungiyar ba wato MLSCN.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci