OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

Gwamnatin Tarayya tace za'a fara shigo da kayan abinci ba tare da biyan haraji ba

Gwamnatin Tarayya tace za'a fara shigo da kayan abinci ba ta

Gwamnatin Tarayya ta ce daga mako mai zuwa za'a fara aiwatar da umarnin da ta bayar, na dakatar da karɓar haraji a kan kayayyakin abinci da ake shigar da su ƙasar nan daga waje.

 

Shugaban Hukumar hana fasa kwauri ta kasa Bashir Adeniyi ya sanar da hakan, a yayin taron Shugabannin hukumomin tsaro da aka yi a Abuja, inda ya ce za'a fara aiwatar da shirin da zarar an kammala tsara ka'idojin da aka shimfiɗa.

 

A cewar Bashir ana fayyace ƙa'idojin a ma'aikatar kuɗi, kuma ya tabbatar da cewa zuwa mako mai zuwa za'a kammala fitar da ƙa'idojin.

 

A ƙarshe ya bada tabbacin cewa tuni wasu daga cikin kayan sun riga sun shigo kasar nan, kuma za'a fitar da su ba tare da biyan haraji ko kuɗin fito ba.

 

Tun a watan Yuli ne gwamnatin ta sanar da cewa ta amince da wa'adin kwana 150 na shigar da Masara da Shinkafa da kuma Alkama daga waje ba tare da biyan haraji ba, domin magance matsalar tsadar kayan abinci a ƙasar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci