OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Amince Da N514m Na Aikin Lantarki A Karkara

Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Amince Da N514m Na Aikin Lantarki

Majalisar zartaswar jihar Bauchi ta amince da kashe Naira miliyan 514 don aikin samar da wutar lantarki a yankunan karkara.

Za a yi amfani da kudin ne wajen siyan tiransfoma da igiyoyin wuta domin gudanar da aikin a yankunan karkara na jihar.

Haka kuma Ma’aikatar wutar lantarki da kimiyya da fasaha ta jihar Bauchi ce za ta gudanar da aikin.

Kwamishiniyar wutar lantarki, kimiyya da fasaha a jihar, Maryam Garba Bagel ce ta bayyana hakan.

Bagel ta bayyana cewa, za a cire Naira miliyan 319 daga cikin kudin domin sake hade garuruwa 37 da cibiyar wutar lantarki ta kasa.

Ta kara da cewa garuruwa 200 ne za su ci gajiyar sayan taransfoma na Naira miliyan 195 da suka hada da sauran kayayyakin aiki.

Yayin da ta lura cewa wasu daga cikin garuruwan da za su ci gajiyar aiyukan sun kasance cikin duhu na tsawon shekaru biyu zuwa goma, haka kuma hanyoyin da aka sanya don aiwatarwa za su taimaka wa gwamnati wurin rage farashi.

Har ila yau, majalisar ta kuma amince da gina titunan karkara na Naira biliyan 20 a fadin kananan hukumomin hudu na jihar.

Hanyoyin da zasu ci moriyar aiyukan sun hada da titin Miya zuwa Soro na karamar hukumar Ganjuwa, titin Rishi zuwa Tulu zuwa Tama a karamar hukumar Toro da hanyoyin da suka hada Rimin Zayam zuwa Polchi, sai kuma Misau zuwa Miya da suka hada kananan hukumomin Misau da Ganjuwa.

Sauran hanyoyin da majalisar ta amince da su sun hada da gyaran hanyar Maraban Liman Katagum da sauran hanyoyin garin Azare da ke da tsawon sama da kilomita 200.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai