Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da shirinta na kafa Hukumar kula da masu bukata ta musamman. An amince da hakan ne bayan Majalisar Dokokin Jihar ta gudanar da taron jin ra’ayin al’umma, kuma kudurin ya tsallake karatu na biyu.
Hukumar kula da masu bukata ta musamman za ta taka muhimmiyar rawa wajen kare hakkokinsu, da kuma ba su damar shiga a dama da su kamar kowa da nufin samar da daidaito a cikin al’umma.
Kafa hukumar zai kawar da nuna wariya ga nakasassu da kuma tabbatar da cewa suna da damar samun ilimi, kula da lafiya, da kuma aikin yi kamar kowa.
A lokacin taron jin ra’ayin jama’ar, kakakin majalisar dokokin jihar, Alhaji Abubakar Mohammed Luggerewo, ya jaddada irin tasirin da dokar za ta yi inda yace gwamnati za ta samar da tallafi na gaggawa ga wadanda suke bukata kuma ta kirkiro da tsari mai dorewa na dogon lokaci na ci gaba da hada kowa da kowa.”
Dan Majalisar yankin Kwami, Shu’aibu Adamu Haruna, shi ne ya dauki nauyin kudurin dokar Hukumar Nakasassu yana mai cewa a yi saurin amincewa da ita don sa hannun Gwamna.
Tun farko a jawabinsa, Shugaban Kwamitin Majalisa Kan Harkokin Mata da Ayyuka na Musamman, Gabriel Galadima Fushison, ya ba wa takwarorinsa da sauran masu ruwa da tsaki da suka goyi bayan wannan tsari.
Dan majalisar ya tabbatar da cewa kwamitinsa zai yi aiki tukuru don tabbatar da fara aiki wannan hukuma.
0 Tsokaci