OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

Gwamnan Gombe yace bazai iya biyan sabon Mafi karancin albashi ba

Gwamnan Gombe yace bazai iya biyan sabon Mafi karancin albas

Gwamnan Gombe Inuwa Yahya, ya ce gwamnatinsa ba za ta iya biyan sabon mafi karancin albashi na Naira dubu saba’in ga ma’aikatan jihar ba.

 

Yayin wani taro da shugabannin kwadago, da kungiyoyin farar hula, da yan kasuwa a gidan gwamnati a jiya Talata, ya ce kason da jihar Gombe ke samu daga asusun tarayya ba zai iya aiwatar da karin albashin ba.

 

Inuwa Yahya ya ce hatta mafi karancin albashin dubu talatin na baya na da kalubale ga gwamnatocin jihohi da dama wajen aiwatar da shi.

 

Dangane da batun zanga-zanga da wasu matasan kasar nan ke shirin gudanarwa daga gobe Alhamis kuwa, Gwamnan ya bukaci mazauna jihar su kauce mata, yana mai gargadin cewa, za ta iya haifar da tashin hankali da barna.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci