OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnan Gombe Ya Yi Kira Da a Tallafa Wa Zaurawa Da Marasa Galihu

Gwamnan Gombe Ya Yi Kira Da a Tallafa Wa Zaurawa Da Marasa G

Governor Muhammadu Inuwa Yahaya| Photo Source: ThisNigeria

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi kira da a tallafa wa zaurawa da wadanda suka rasa mazajen su a hanyar neman zaman lafiya.

Gwamnan ya jaddada muhimmancin yin hakan ne a ranar Alhamis a Abuja.

Hakan ya zo ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar kan harkokin yadda labarai na Gwamnan ya fitar.

Inda ya halarci kaddamar da wani littafi, 'Hawayen Bazawara' wanda Hajiya Hassana Abubakar ta rubuta karkashin kungiyar matan 'yan sanda, gwamnan yace a cigaba da tallafa wa zaurawa.

Wadanda suka halarci taron sun hada da uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari wacce Mrs Lauretta Onochie ta wakilta, da kuma Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, wasu gwamnoni da 'yan majalisar tarayya.

Yahaya ya yaba wa marubuciyar da tayi tunanin bayyana wa jama'a kukan zaurawa don a share mu su hawaye.

Ya kuma yaba wa shugaban kungiyar matan ‘yan sanda da uwargidan IGP, Hajiya Hajara Usman Alkali Baba bisa jajircewar ta da kuma sadaukarwa wanda ya kara karfafa kungiyar wajen cimma manufofinta.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai