OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnan Gombe Ya Tallafa Wa Matasa 500 Da Aiyuka

Gwamnan Gombe Ya Tallafa Wa Matasa 500 Da Aiyuka

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya| Hoto Daga: ThisNigeria

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bawa matasa 500 ayyuka daban-daban domin rage zaman banza.

Gwamnan ya saka matasan cikin shirin gwamnati na tsaro da zirga-zirga da muhalli na jihar Gombe (GOSTEC).

Yahaya ya ce hakan zai rage munanan dabi’u a cikin al’umma.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin da ta gabata yayin da yake ayyana bude horon na tsawon makonni biyu ga wadanda suka ci gajiyar shirin.

Hukumomin da abin ya shafa suna horar da matasan ne a sansanin horar da masu yi wa kasa hidima na NYSC da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe.

Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa wannan ba wa matasa aiki ya yi daidai da manufofin gwamnatin sa na hada kan matasa da rage zaman banza.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati na kokarin baiwa matasa kusan 2,000 aiki tare da hadin gwiwar kungiyar ‘At-Risk Children Project (ARC-P).

Ya kara da cewa duk wadanda suka amfana za a tura su zuwa kananan hukumomi 11 na jihar.

Da yake bayyana irin nauyin da ya rataya a wuyan matasan bayan horar da su, ya ce za su kasance a shirye don tabbatar da dokar zirga-zirga, tsaro da muhalli tare da yin aiki da sauran hukumomin da suke da alaka.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci