OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnan Gombe Ya Raba Wa Matasa Keke Napep 1,000

Gwamnan Gombe Ya Raba Wa Matasa Keke Napep 1,000

Governor Muhammadu Inuwa Yahaya| Photo Source: ThisNigeria

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya raba wa matasa a jihar Keke Napep guda dubu daya. 

Gwamnan ya ce an tallafawa matasan da Keke Napep din ne a matsayin bashi.

Ya kuma kara da cewa tallafin zai tabbatar da rage yawan matasa marasa aikin yi a jihar.

Yahaya ya bayyana cewa an ba da wannan tallafi ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin jihar da kamfanin kera keke Napep din mai suna SIMBA TVS.

Gwamnan ya kara jaddada kudirin sa na rage zaman kashe wando a jihar.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin sa ta bada aiki ga masu samar da ayyukan raya kasa guda 3,000, matasa 27,000 da nufin dashen itatuwa miliyan 4 a jihar sannan kuma an dauki matasa 500 aiki a hukumar tsaro da zirga-zirga da muhalli ta jihar Gombe mai suna GOSTEC.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa za ta bukaci SIMBA TVS ta kafa masana’antar ta a jihar bayan an kammala aikin fagen masana'antu na Muhammadu Buhari wanda ake kan ginawa.

A halin da ake ciki, shugaban kungiyar mahaya Keke Napep, Muhammad Abdullahi Sarki ya nuna jin dadin sa da wannan tallafin.

Ya kara da cewa gwamnan ya zarce adadin Keke Napep da kungiyar ta nema guda 500 ta hanyar ninka ta.

A yayin da yake kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da wannan damar, ya ce gwamnan ya yi nasa bangaren kuma ya kamata a yaba masa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci