OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnan Gombe Ya Amince Da Daukar Malamai 1000, Da Yi Wa 288 Sauyi

Gwamnan Gombe Ya Amince Da Daukar Malamai 1000, Da Yi Wa 288

Governor Muhammadu Inuwa Yahaya| Photo Source: ThisNigeria

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da daukar malamai 1000 aiki a jihar.

Hukumar Kula da Malamai ta Jihar Gombe ce za ta dauki alhakin daukar aikin.

Matakin da gwamnan ya dauka kan daukar ma’aikatan domin a cike gibin da ke tattare da karancin isassun malamai a makarantun gwamnati na jihar ne.

Zaku tuna cewa Gwamnan ya sanya dokar ta baci a fannin ilimi.

Shugabar hukumar kula da ayyukan malamai ta jihar Gombe, Mrs Na'omi Philip Maiguwa ce ta bayyana hakan.

Maiguwa ta bayyana cewa gwamnan ya damu matuka da matsalolin ilimi a jihar musamman karancin malamai a makarantun sakandire na gwamnati.

Gwamnan ya kuma amince da sauya wa ma’aikata 288 na hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar (SUBEB) zuwa makarantun sakandare da kwalejojin fasaha.

Shugabar hukumar ta TSC ta kara da cewa daukar ma'aikatan ya yi fice a matsayin irinsa na farko a jihar.

Ta bayyana cewa a baya babu wani gwamnan jihar da ya dauki malamai har 1,288 aiki, inda ta kara da cewa daukar ma’aikata na karshe a shekarar 2018 an dauki malamai 700 aiki.

Ta ce, “Wannan ci gaban na daya daga cikin matakan da Gwamnan ya dauka na juyar da martabar ilimi a jihar.

“A farkon watan Janairu na wannan shekarar, ya amince ya fara aikin daukar malamai a hukumar ta TSC.

"Wannan amincewan ci gaba ne na sanya kwararrun malamai a makarantun gaba da sakandare na jihar."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci