OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gobara Ta Tashi A Ma'aikatar Kudi Ta Tarayya

Gobara Ta Tashi A Ma'aikatar Kudi Ta Tarayya

Mahukunta sun ce gobarar ba tayi muni ba

Wata Gobara ta tashi a hedikwatar ma'aikatar kudin kasar nan dake babban birnin tarayya Abuja  ta kone abubuwa da dama.

Kawo wannan lokaci ba’a san musabbabin gobarar ba, sai dai tuni ma’aikatan kwana-kwana suka kai agajin shawo kan ta.

Kakakin hukumar kashe gobara ta FCT, Abraham Paul ya ce ma'aikatansu na can suna ƙoƙarin kashe wutar, kamar yadda jaridar punch ta wallafa.

A wani saƙo da ma'aikatar kuɗi da kasafin ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce gobarar ba ta yi muni ba kamar yadda aka yi ta zuzutawa a shafukan sada zumunta inda ta ce wasu batira ne da aka keɓe suka kama da wuta a wani zaure da ke ƙasa a cikin hedikwatar ma'aikatar.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci