OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

FCTA Ta Rusa Masallaci Da Islamiyya a Abuja

FCTA Ta Rusa Masallaci Da Islamiyya a Abuja

FCTA

Hukumar babban birnin tarayya Abuja (FCTA) ta rusa wani masallaci da Islamiyya wanda aka gina a filin da aka haramta gini akai a kauyen Zauda da ke unguwar Jiwa na Abuja.

Tawagar FCTA karkashin jagorancin babban mataimaki na musamman ga ministan Abuja akan sa ido da tabbatar da aiki, Ikharo Attah ne suka rusa gine-ginen a ranar Litinin.

A yayin aikin rushewar, Attah ya ce: "Muna so mu yi kira ga mutane da su fahimci cewa ''haramci ya cigaba da zama haramci', ba mu saba wa mahalicci ba.

"Lokacin da muka zo nan a yau, mun gano cewa an gina wata cibiyar ibada a kan haramtaccen fili, kuma za mu cire su."

“Ba za a biya diyya ga masu gine-ginen ba.

“Babu wani diyya da aka ware wa wannan yanki kwata-kwata.

"Shugabannin kauyen duk suna nan duk da cewa mutanen sun yi zargin cewa sun sayar musu da filayen."

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Daraktan FCTA, sashen kula da ci gaban kasa, Muktar Galadima ya ce sama da gidaje 500 da wuraren ibada da kuma dakunan ajiya ne aka rushe a yankin.

A cewar sa: “Wannan shi ne ci gaba da abin da muka fara kwanaki biyu da suka gabata, na ruguje haramtattun gine-gine a kan hanyoyin samar da ababen more rayuwa, yau mun zo kammala shi.

“Ya zuwa yanzu, daga ranar Juma’a, 23 ga watan Satumba, zuwa yau, an cire gine-gine sama da 500.

"Mun ba su damar cire kayan su masu daraja."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci