OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Fadan Sojoji Da 'Yan Sanda a Jihar Adamawa Yayi Sanadiyar Rasa Rai

Fadan Sojoji Da 'Yan Sanda a Jihar Adamawa Yayi Sanadiyar Ra

Biyo bayan wani fada da ya barke tsakanin jami'an 'yan sandan Najeriya da sojoji a hanyar Numan a jihar Adamawa, soja daya ya mutu.

Fadan da ya kai ga yin musayar wuta ya yi sanadiyar mutuwar sojan da ke bakin aiki.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda a Yola, DSP Sulaiman Nguroje, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sikiru Akande ya bayar da umarnin cafke ‘yan sandan da lamarin ya shafa.

Nguroje ya kara da cewa kwamishinan ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Ya kuma ba da tabbacin cewa za a yi adalci a karshen binciken.

Kwamishinan ya nuna rashin jin dadin sa game da wannan mummunan lamari inda ya kara da cewa ba za a sake lamuntar harin da ake kaiwa jami'an tsaro ba.

CP Akande ya kara jaddada kudirin rundunar ‘yan sandan na kare rayuka da dukiyoyin jama’a inda ya kara da cewa akwai bukatar a hada kai da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da jami’an da ke gudanar da ayyukan su.

Kwamishinan ya kuma yi kira da a kwantar da hankula tare da tabbatar da cewa duka jami'an tsaron da abin ya shafa suna yin duk abin da ake bukata bisa doka don tabbatar da an yi adalci.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci