OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

El-Rufa'i Ya Yi Tankade Cikin Gwamnatin Sa, Ya Bada Sabbin Mukamai

El-Rufa'i Ya Yi Tankade Cikin Gwamnatin Sa, Ya Bada Sabbin M

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i| Hoto Daga: BBC

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya yi tankade cikin gomnatin sa, tare da sanya sabbin mukamai ga wasu kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatin jihar.

Sauyin ya faru ne a yau, Talata, inda gwamnan ya bayyana cewa an tsara sauye -sauyen ne don tallafawa da kuma amfani da sabon tsari don cin nasara a tafiyar karshe na gwamnatin.

Ya kara da cewa hakan zai kawo sabbin fahimta da nunin baiwa tare da bawa kwamishinonin damar samun karin gogewa a aiyukan gwamnatin.

Wata sanarwa da mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye ta fitar ta bayyanin cewa kwamishinoni takwas daga cikin 14 ne sauyin ya shafa.

Muyiwa ya bayyana cewa canjin bai shafi ma'aikatun kudi, shari'a, lafiya, gidaje da raya birane, tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida da ayyukan dan adam da ci gaban zamantakewa ba.

A cewar sanarwar, Muhammad Sani Abdullahi, Shugaban Ma’aikata, ya koma kwamitin tsare-tsare da kasafin kudi, nauyin da “ya rike da banbanci a lokacin wa’adin farko na Malam El-Rufai. Wannan shi ne karo na biyu da ake mayar da wani babban ma’aikacin gwamnan a matsayin Kwamishina."

Sanarwar ta kara da cewa: “Sabbin mukamai na kwamishinonin da aka sauya wa aiki sune: Muhalli: Jaafaru Sani; Ayyukan Jama'a: Thomas Gyang; Ilimi: Halima Lawal; Aikin Noma: Ibrahim Hussaini; Kananan Hukumomi: Shehu Usman Muhammad; Hukumar tsare -tsare da kasafin kudi: Muhammad Sani Abdullahi; Kasuwanci, Kirkiro da Fasaha: Kabir Mato, Ci gaban Wasanni: Idris Nyam."

Sanarwar ta kara da cewa: "Malam Nasir El-Rufai ya isar da godiya ga gwamnatin jihar kan hidimar Aliyu Saidu, tsohon DG-KADCHMA da Lawal Jibrin, tsohon GM na KEPA, wadanda ke barin gwamnati."

Jihar Kaduna tana daya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da take samun sauyi na gyara da gomnati ke yi kan ayyukan muhalli, ilimi, lafiya da sauran su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci