Jami'an tsaro sun kama 'yan ƙasar Poland bakwai bisa zargin ɗaga tutocin Rasha yayin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihar Kano.
Kakakin rundunar tsaron farin kaya, Peter Afunanya, ya faɗa yayin taron manema labarai a yau Laraba cewa sun kama su ne lokacin da jami'ansu ke ƙoƙarin tabbatar da tsaro.
Sai dai bai yi ƙarin bayani ba game da ko su wane ne, yana mai cewa amma ba farautar 'yan ƙasar ta Poland a Najeriya suke yi ba.
Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito jakadan Poland a Najeriya, Stanislaw Gulinski, yana tabbatar da kamen yayin ganawar da jakadu suka yi da gwamnatin Najeriya ranar Laraba a Abuja.
"An kama su kwana biyu da suka wuce a Kano, abu na ƙarshe da na ji shi ne ana shirin kawo su Abuja a jirgi," in ji shi.
Sai dai ya ƙi yin ƙarin bayani lokacin da Reuters ya tuntuɓe shi.
0 Tsokaci