OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Daliban Jami'ar Tarayya, Lafia Sun Kubuta Daga Hannun 'Yan Bindiga

Daliban Jami'ar Tarayya, Lafia Sun Kubuta Daga Hannun 'Yan B

Federal University Lafia

Hukumar gudanarwar Jami’ar Tarayya, Lafia (FULafia) ta sanar da bayyana cewa daliban ta  hudu da wasu ‘yan bindiga suka sace a ranar 13 ga watan Janairu sun samu kubuta.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na jami’ar, Abubakar Ibrahim ya fitar ranar Lahadi a Lafiya ta ce an sako daliban ne a yammacin ranar 15 ga watan Janairu.

Sanarwar ta ce shugaban jami’ar, Farfesa Shehu Abdul-Rahman, ya mika godiyarsa ga gwamnatin jihar da sauran jama’a bisa gudunmawa da addu’o’i da kuma goyon bayan da suka bayar a wannan lokaci.

Ya kuma godewa jami’an tsaro kan yadda suka dauki matakin da ya sa aka dawo da daliban cikin gaggawa.

Shugaban jami’ar ya kuma haori daliban da su kwantar da hankulan su, su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum a harabar jami’ar kamar yadda aka saba, inda ya bayar da tabbacin jajircewar  wajen samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyi a cikin harabar jami’o’in da kewaye.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai