OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

DA DUMI-DUMI: Kisan Makiyaya Biyu Ya Jefa Jama'a Cikin Firgici a Lafiya

DA DUMI-DUMI: Kisan Makiyaya Biyu Ya Jefa Jama'a Cikin Firgi

Hoto Daga: PremiumTimes

Sakamokon kisa da aka yi wa wasu makiyaya biyu a garin Ashige da ke karamar hukumar Lafiya a jihar Nasarawa, jama'a na zaman dar-dar.

Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan bindigan da ba'a san ko su waye ba ne suka kashe makiyayan.

An tsinci gawarwakin ne a cikin wata gona tare da raunin yanka daban-daban a fuskokin su.

Lamarin da ya faru a daren jumma'a dai ya jefa mutane cikin firgici.

Tuni aka kai gawarwakin asibitin kwararru na Dalhatu A`râf dake garin na Lafia.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci