OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

DA DUMI-DUMI: Babu Maganar Dage Taron APC Na Kasa- Gwamnonin APC

DA DUMI-DUMI: Babu Maganar Dage Taron APC Na Kasa- Gwamnonin

Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun jaddada cewa za a gudanar da babban taron jam’iyyar a watan Fabrairu kamar yadda aka tsara.

Gwamnonin sun dauki matakin ne a wani taro da suka yi a daren Lahadi a Abuja.

Shugaban kungiyar Gwamnonin Kuma Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ne ya bayyana wa manema labarai hakan.

Bagudu ya bayyana cewa, an kada kuri'ar amincewa da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a cikin kwamitin riko ciki har da wasu mutane biyu.

Sauran biyun sun hada da Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja da Gwamna Gboyega Oyetola na jihar Osun.

 

Taron wanda ya gudana a masaukin Gwamnan jihar Kebbi ya samu halartar gwamnonin APC kusan 20.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci