OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Buhari Ya Yi Tir Akan Barkewan Sabon Rikicin Jihar Filato

Buhari Ya Yi Tir Akan Barkewan Sabon Rikicin Jihar Filato

Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna rashin jin dadin sa game da sake barkewar kashe-kashe a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Shugaban ya bayyana lamarin a matsayin ramuwar gayya kuma ba za a amince da shi ba.

Ya ce sabon harin bai dace da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin Fulani da Irigwe a cikin garin na Bassa ba.

Shugaban ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka rasu.

Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Shugaban ya ce: “Kowace bangare da ke daukar doka a hannun ta na ikirarin ramuwar gayya ce. A matsayin al'umma, babu mazaunin irin wannan tashin hankalin. Wannan ba abin yarda ba ne."

Ya kuma bayyana jin dadinsa kan yadda gwamnatin jihar ke kokarin magance rikicin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci