OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Buhari Ya Isa Jihar Ebonyi Ziyarar Aiki

Buhari Ya Isa Jihar Ebonyi Ziyarar Aiki

Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka a Jihar Ebonyi a wata ziyarar aiki ta kwana biyu da yake yi.

Rahotanni sun bayyana cewa Shugaban ya sauka a Babban Filin Jirgi na Akanu Ibiam da ke Jihar Enugu, inda ya karasa zuwa Uburu da ke karamar Hukumar Ohanzara a Jihar Ebonyi.

Gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi da takwaransa na Ebonyi David Umahi ne suka tarbi shugaban tare da sauran manyan jami’an gwamnati.

Ana sa ran Buhari zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Umahi ta aiwatar, wanda yanzu haka yake neman jam'iyyarsu ta APC ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa titunan jihar sun cika da jami’an tsaro, wanda ake sa ran baya rasa alaka da yadda kungiyar aware ta IPOB ke gudanar da ta’addanci a yankin a kokarin su na ficewa daga tarayyar Najeriya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci