OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Buhari ya ba da umarnin bude masana'antar siminti na Dangote da ke jihar Kogi

Buhari ya ba da umarnin bude masana'antar siminti na Dangote

Muhammadu Buhari

Kwamitin tsaro na kasa (NSC) karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin bude kamfanin siminti na Dangote da ke Obajana a jihar Kogi da gaggawa.

Majalisar ta bayar da umarnin ne a wani taro da ta gudanar a zauren majalisar dokokin jihar da ke Abuja.

Ministan harkokin ‘yan sanda, Mohammed Dingyadi, tare da takwaran sa , Rauf Aregbesola da babban hafsan tsaron kasa (CDS), Janar Lucky Irabor, sun bayyana wa manema labarai kadan daga cikin abinda aka tattauna a taron.

Aregbesola ya ce an cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar Kogi da kamfanin Dangote kan bukatar sake bude masana’antar siminti, inda aka bukaci  bangarorin biyu su sanya hannu a bisa yarjejeniyar.

Ministan ya kara da cewa majalisar ta ba da umarnin bude masana’antar da gaggawa  tare da ba da shawarar cewa  duk wasu batutuwan da ake takaddama a kai a war ware bisa tsarin doka, domin gwamnati ta himmatu wajen samar da ayyukan yi.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci