OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Watanni da suka shude

Buhari Bai Yi Abin Azo A Gani Ba, Cewar Jam'iyyar LP  

Buhari Bai Yi Abin Azo A Gani Ba, Cewar Jam'iyyar LP  

Shugabancin jam’iyyar Labour Party ya yi kaca-kaca da gwamnatin Buhari na barin talakawa a cikin halin wahala.

Shugaban na LP yace babu abin da akayi bare su yi murnar cikar ƙasar shekaru 62 da samun ƴancin kai.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na kasa Abayomi Arabambi ya fitar a Abuja.

Arabambi ya ce ga kasar da ta keyin bikin cikan ta shekaru 62 da samun mulkin kasar, a fili yake cewa gwamnatin Buhari ta rashin gaskiya ta yi nasarar dora kasar a kan turba marar kyau.

Bala'i ne zaɓen jam'iyyar APC a ƙasar nan, hakan ya baiwa APC damar sanya ƙasar a hanyar cin hanci da rashawa, rashin inganci, da kuma rashin tsaro, in ji shi.

A cewarsa, ƙasar nan ba ta da wani abu na tarihi da APCn tayi cikin shekaru bakwai, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ƙasar ba ta da wani abu da za ta yi murna a kai, a maimakon haka mafi yawan al’ummar da ke fama da matsananciyar wahala suna danasanin zaɓan APC.

“A kusan dukkan ɓangarorin mulkin ƙasa, APC  bata samu maki ko da ɗaya ba, A harkan ma sifili za'a bata.

"Ilimi ma babu ko maki ɗaya, haka a fannin kiwon lafiya, babu wani sashe ɗaya da da akaci nasara a gwamnatin APC".

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai