OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Bishop Kukah Yayi Tir Da Kisan Da Aka Yi A Sokoto, Yace Bata Da Alaka Da Addini

Bishop Kukah Yayi Tir Da Kisan Da Aka Yi A Sokoto, Yace Bata

Bishop Mathew Hassan Kukah| Photo Source: Daily Post

Bishop Mathew Hassan Kukah na shiyyar Sokoto ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da aka yi wa wata daliba bisa zargin batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) a jihar.

Dalibar 'yar aji biyu ce a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto inda take karantar Home Economics.

An kashe ta ne ta hanyar kona ta da safiyar ranar Alhamis bayan da aka yi mata dukan da ta fita hankalin ta. 

Bishop Kukah yayi Allah wadai da wannan aika aika tare da nesanta shi da addini.

Ya bayyana cewa Musulmi da Kirista a jihar sun dade suna zaman lafiya.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Sokoto.

Sai dai ya danganta lamarin a matsayin laifi yayin da yake kira ga jami’an tsaro da su gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aikan.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Na ji matukar kaduwa da labarin irin wannan mummunan lamari da ya faru a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, wanda ya kai ga kisan gillar da aka yi wa Misis Deborah Yakubu, dalibar aji biyu a fannin Home Economics a yau.

“Muna yin Allah wadai da wannan lamari da kakkausar murya, muna kuma kira ga hukumomi da su binciki wannan mummunan lamari tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk wadanda suka aikata laifin.

“Abin da kawai ya rataya a wuyan danginta, sauran dalibai da kuma hukumomin makarantar shi ne tabbatar da cewa duk wanda ya aikata wannan ta’asa, ko menene ya tunzura shi, ana hukunta shi ne bisa ga sauran dokokin kasarmu.

Yayin da yake lura cewa aika-aikan ba na addini ba ne yace, “Wannan ba ruwansa da addini. Kiristoci sun zauna lafiya da makwabta musulmi a nan Sokoto tsawon shekaru. Dole ne a dauki wannan al'amari a matsayin wani laifi kuma dole ne doka ta dauki dalilinsa."

Ya kuma yi kira ga al’ummar Kirista da su kwantar da hankalinsu tare da aika addu’o’in su ga Deborah, wacce aka kashen.

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta kuma sanar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci