OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

Bata gari sun wawashe ofishin NCC a Kano

Bata gari sun wawashe ofishin NCC a Kano

Wasu bata-gari sun far wa ofishin Hukumar Sadarwa ta Kasa NCC da ke Kano inda suka kwashe kwamfutoci da kujeru wasu kayan aiki na dumbin miliyoyin Naira.

Masu tarzomar sun kuma cinna wuta a ofishin kafin daga bisani jami’an tsaro su kawo dauki a wurin.

Tun da farko ‘yansanda sun tarwatsa wasu matasa da suka kunna wuta a kofar gidan gwamnatin Kano.

Wannan dai na zuwa a daidai lokacin da al'umma suka fito yin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin kasarnan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci