OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Babu Zancen Komawa APC A Yanzu— Kwankwaso

Babu Zancen Komawa APC A Yanzu— Kwankwaso

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso| Hoto Daga: Leadership

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa bashi da Wani Shiri na barin jam’iyyar sa ta PDP Zuwa Jam’iyyar APC Mai Mulkin Nigeria.

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne Cikin Wata Hira da yayi da Gidan Radio na DW dake Kasar Jamus.

Gidan Radio ya rawaito Sanata Kwankwaso ya na cewa a a yanzu dai bashi da Wata niyya ta barin jam’iyyar PDP Zuwa APC Kamar yadda ake ta jita-jitar zai bar jam’iyyar.

Sanata Kwankwaso ya ce tasirin sa. Siyasar Kano ta sa wasu ke yaɗa jita-jitar a fatan su na ganin sun yi aiki tare.

Idan za’a iya tunawa an fara tunani Kwankwaso da Ganduje zasu yi Sulhu ne tun bayan da Gwamna Ganduje ya Kaiwa Sanata Kwankwason Ziyarar ta’aziyyar kaninsa da ya rasu a kwanakin baya.

Kan batun tsayawa takarar shugabancin ƙasa nan kuwa Kwankwason ya ce suna tattaunawa da masu ruwa da tsaki kafin su ɗauki matsayar karshe kan lamarin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci