OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 10 Watanni da suka shude

Babbar Motar Ta Murƙushe Mutane Uku Har Lahira a Ogun

Babbar Motar Ta Murƙushe Mutane Uku Har Lahira a Ogun

Wata babbar mota ta murƙushe matafiya uku har lahira tare da raunata wasu a wani hatsarin da ya afku a unguwar Obada da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Wakilin Jaridar Punch ya tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 07:15 na safe, a kusa da ofishin ƴan sanda na Obada da ke kan hanyar Legas zuwa Abeokuta.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, kakakin hukumar kiyaye haɗurra ta tarayya a jihar Ogun, Florence Okpe, ta ce manya maza biyar ne hatsarin ya rutsa dasu.

Ta ce, “Mutane biyu sun samu raunuka kuma abin takaici, mutane uku sun mutu."

Ta ƙara da cewa motocin da abin ya shafa sune karamar mota kirar Volvo mara lamba da tasi da kuma mota kirar Nissan mai lamba AKM489ZY.

Okoe ya ce, "Abinda ake zargin ya haddasa hatsarin saɓawa dokan hanya ne daga ɓangaren direban babbar mota yayin da ya yi karo da motar Nissan."

Ta ce an kai waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Abeokuta domin kula da lafiyarsu.

Yayin da aka ajiye gawarwakin waɗanda suka mutu a ɗakin ajiyar gawa na asibitin.

A halin da ake ciki, kwamandan hukumar FRSC reshen Ogun, Ahmed Umar, yayin da yake jajantawa iyalan waɗanda haɗarin ya rutsa da su, ya shawarci masu ababen hawa da su guji saɓawa dokokin hanya.

Mista Umar ya ƙara da cewa, tsaro aikin kowa ne, musamman a wannan lokacin da ake yawan zirga-zirgar ababen hawa, yana mai cewa, “kowa ya kamata ya tuƙa mota cikin taka-tsantsan da bin ƙa’idojin zirga-zirga.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai