Sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu, Sanata Ifeanyi Uba ya mutu a birnin Landan.
Sanata Ubah wanda dan jam’iyyar APC ne ya rasu a dakin otal dinsa kwanaki biyu bayan ya bar kasar nan.
Marigayin ya mutu a safiyar yau Asabar biyo bayan rashin lafiya da ta yi kamari a cikin kwanaki biyu.
An ruwaito cewa kafin ya koma ga mahalicci da ‘yan kwanaki kadan, ya bayar da gudunmawar Naira Miliyan 71 domin karfafawa jami’iyyar a shirinsu na samun nasara a zaben gwamna da za a yi a jihar.
0 Tsokaci