OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

"Ba muji dadin karin kudin abinci ba" -Gwamnatin Kano

Governor Yusuf of Kano

Gwamnatin Kano ta nuna rashin Jin dadinta ga ‘yankasuwa bisa hauhawar farashin kayan abinci a kasuwannin jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da gwamnatin jihar ta yi da manya da kananan ‘yankasuwa Wanda a ka gudanar a gidan gwamnatin jihar.

Gwamna Yusuf ya ce gwamnatin Kano a shirye take domin ta hada Kai da ‘yankasuwa domin farfado da tattalin arzikin kasuwannin jihar.

Gwamna Yusuf ya Kuma nuna rashin Jin dadinsa bisa yadda Wasu matasa suka yi amfani da harkar zanga-zanga suka sacewa wasu ‘yankasuwa kayansu na kasuwanci.

Shima a nasa jawabin shugaban ‘yankasuwa na jihar Kano Alhaji Sabi’u Bako ya godewa gwamnatin jihar Kano bisa namijin kokari da gwamnati ta yi wajen Samar da tsaro a manyan kasuwannin jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci