OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Ba Kasar Da Za Ta Ci Gaba Ta Tare Da Kimiyya Da Fasaha Ba— Ganduje

Ba Kasar Da Za Ta Ci Gaba Ta Tare Da Kimiyya Da Fasaha Ba—

Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, and Minister of Science,Technology and Innovation, Dr.Ogbonnaya Onu


Gwamnatin Kano ta ce babu kasar da zata samu ci gaba cigaba idan ba ta mayar da hankali kan kirkire kirere da amfani da kimiya da fasaha ba .

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a wajen taron majalisar kula da kimiya da fasaha ta kasa karo na 20 Wanda aka gudanar a Abuja da hadin guiwar Ma'aikatar Kimiya da fasaha ta kasa da kuma gwamnatin jihar Kano.

Gwamnan, wanda Mataimakinsa, Dr Nasiru Yusuf Gawuna wakilta, ya ce  duk kasar da bata rungumi  kirkire kirkire ko kimiya da fasaha ba, to zata zama mai dogaro ga wasu kasashen.

Dr Gawuna yace Najeriya bata cikin jerin irin wadannan kasashen na  duniya, inda a yanzu ta shiga cikin jerin kasashe 20 da suke iya tafiyar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da ta dogara da wata kasa ba, inda ake sa ran matsayin na ta zaifi haka nan zuwa  2030.

Cikin wata takarda da Daraktan yada labarai na Mataimakin gwamnan Kano Hassan Musa Fagge ya fitar , yace a nasa jawabin , ministan kimiya da Fasaha na kasa Dr Ogbonnaya Onu yace tsawon shekaru gwamnatin tarayya tana bada mahimmacin ga majalisar kula da kimiya da fasaha ta kasa domin samun abinda ake so na cigaban kasa .

Yace daga cikin abinda gwamnatin tarayya ta amfana da irin wannan shiri shine tana Sanin abinda ke faruwa a jihohin Najeriya.

Ministan ya Kuma yabawa gwamnatin jihar Kano abisa shirya taron .

Taken taron na bana karo na 20 shine cigaban Najeriya ya taallaka ne da kimiya da fasaha da Kuma kirkire kirkire.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci