OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Atiku Ya Kai Ziyara Ondo, Yace APC Ce Ta Raba Kan 'Yan Najeriya

Atiku Ya Kai Ziyara Ondo, Yace APC Ce Ta Raba Kan 'Yan Najer

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ziyarci jihar Ondo a ci gaba da tuntubar da yake yi.

Atiku ya kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki da kawo rabuwar kai a kasar.

Ya ce rashin adalcin da gwamnatin APC karkashin jagorancin Buhari ta yi wa dukkan sassan kasar nan ya kawo illa ga hadin kan kasar.

Ya koka cewa kasar ba ta taba ganin irin rashin hadin kai na yanzu ba tun da aka kirkiro ta.

Ya kuma jaddada cewa matsalolin Najeriya za a iya magance su ne kawai idan kasar ta kasance a dunkule.

Tsohon Mataimakin ya yi alkawarin yin aiki da kowa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasar.

Ya kara da cewa yin aiki a matsayin Najeriya daya zai ba shi damar kawo karshen ta'addanci da sauran matsalolin da suka addabi kasar.

Ya kuma jaddada bukatar sake fasalin kasa tare da bayyana cewa gwamnati mai ci ta mayar da sassan kasar baya.

Atiku ya ce, “Gwamnatin APC ta haifar da rashin hadin kai da ban taba gani ba a rayuwata a kasar nan. Idan aka zabe ni zan sake hada kan kowane bangare na kasar,” kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi kowa cancantar ceto kasar nan daga halin da take ciki.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci