Rahotanni na cewa an cinna wuta a hedikwatar jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Jigawa.
An banka wa babban ofishin jam’iyyar wuta a yayin da zanga-zangar matsin rayuwa ta rikide ta koma rikiciwasu fustattun matasa ne suka far wa ofishin jam’iyyar da ke birnin Dutse, inda suka lalata allunan da ke dauke da tambarin jam’iyyar da hotunan wasu ’ya’yanta gabanin cinna wa ginin wuta.
Kazalika, matasan sun kone wasu motoci da suka tarar ajiye a harabar ginin jam’iyyar.
Wannan tarzoma dai ta yadu a wasu sassan jihar inda matasa dauke da makamai ke cin karensu babu babbaka duk da kokarin da jami’an tsaro ke yi na yi wa tufkar hanci.
A Birnin Kudu, an lalata tare da wawushe dakin ajiyar hatsi da takin zamani na gwamnatin jihar, yayin da wasu bata-garinsuka far wa kamfanin noma na JASCO da ke garin Gumel.
Bata-garin sun kuma kai farmaki gidan dan majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gumel, Gagarawa da Maigatari da kuma gidan mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar ta Jigawa
0 Tsokaci