Aƙalla mutum 31 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon ambaliyar ruwa a ƙananan hukumomin jihar Kano 21.
Babban sakatare na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kano, Isyaku Kubarachi, ya ce ambaliyar ta kuma rusa gidaje 5,280 a jihar.
"Mutum 31,818 lamarin ya shafa da kuma rusa gidaje 5,280," in ji shi. "Bala'in ya kuma lalata gonaki 2,518 da suka kai faɗin hekta 976."
Ya ce ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ne ya jawo ambaliyar, kuma akasarin gidajen da lamarin ya shafa na ƙasa ne.
Kubarachi, ya ce hukumar ta gabatar da wani shiri ga gwamnatin jihar don samar da kayan tallafi ga magidantam da lamarin ya shafa.
Ya kuma jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki matakan kariya kafin saukar damina don kare rayuka da dukiyoyi.
Hakazalika, yace a halin yanzu suna kokarin ganin an tallafawa wadanda lamarin ya shafa.
0 Tsokaci