OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Almubazzaranci Ne Gina Cibiyar Taro Ta N5bn a Gombe, Cewar Inuwa Yahaya

Almubazzaranci Ne Gina Cibiyar Taro Ta N5bn a Gombe, Cewar I

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya| Hoto Daga: ThisNigeria

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya caccaki tsohuwar gwamnatin jihar akan gina cibiyar taro ta N5bn.

 

Yahaya ya ce almubazzaranci ne da dukiyar jama'a ganin cewa ba'a amfani da cibiyar.

 

Hakan ya zo ne cikin jawabin sa a wani taro da mazauna jihar kan shirye-shiryen kasafin kudin shekarar 2022.

 

Ya kara da cewa aikin da tsohuwar gwamnatin ta gudanar bata cancanci a kashe wannan makudan kudaden ba.

 

Ya ce jihar ba ta bukatar wata cibiyar taro yayin da take da Jewel Hall, wanda a halin yanzu yana amfani iri daya tun 1972.

 

Gwamnan ya bayyana cewa har yanzu cibiyar na bukatan naira miliyan 500 don sayan kujeru da sauran kayayyaki da zasu sa ta fara aiki.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci