OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ahmed Lawan Ya Karbi Fom Na Naira Miliyan 100 Na Takarar Shugabancin Najeriya

Ahmed Lawan Ya Karbi Fom Na Naira Miliyan 100 Na Takarar Shu

Senate President, Ahmed Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya shiga jerin sunayen masu takarar neman shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.

Lawan wanda shi ne na 24 a jerin sunayen ya karbi fom din sa a yau (Litinin) gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar da ke tafe a karshen watan nan.

Abokan siyasar sa karkashin jagorancin daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC na kasa, Cif Sam Nkire ne suka karbi fom din a madadin shugaban majalisar dattawan.

Nkire tare da wasu Sanatoci 15 ya ce Najeriya na bukatar shugaban kasa wanda zai yi aiki ba tare da kabilanci ba.

Ya bayyana cewa, “Muna son Shugaban Majalisar Dattawa na yanzu ya zama Shugaban Najeriya saboda dalilai da dama.

“Tsarin zaman lafiyar kasa daya, kuma shugaban da muke kawowa al’ummar Najeriya shugaban Najeriya ne, ba shugaban Igbo ba, ba shugaban Fulani ba, ba shugaban Yarbawa ba, shugaban Najeriya ne wanda muka zuba ido muka ga cewa ya cancanta, babu wani dan takara da zai kasance mai kishin kasa kuma wanda ke da ra’ayin talakawan Najeriya kamar shi,” kamar yadda AllNews ta tattaro.

Ya ci gaba da cewa shugaban majalisar dattawan ya aminta da karbar fom a madadin sa bayan abokai da ‘yan’uwa da abokan siyasa sun bayar da gudunmawar sayen fom din.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci