OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Abin Tausayi: Kwale-kwale Ya Kife Yayin Da 18 Suka Mutu a Katsina

Abin Tausayi: Kwale-kwale Ya Kife Yayin Da 18 Suka Mutu a Ka

Photo Source: Legit Hausa

Akalla mutane 18 ne wanda akasari yara ne suka rasa rayukansu sakamakon kifewar wani jirgin ruwa da ke dauke da su a Katsina.

Lamarin dai ya faru ne a karamar hukumar Mai’adua ta jihar Katsina.

A lokacin tattaro rahoton nan an ba da sanarwar bacewar wasu mutane shida Wanda lamarin ya shafa.

Yayin da ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah ba, AllNews ta tattaro cewa wani Lawal Sakatare ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin.

Sakatare ya bayyana cewa mutane 24 ne ke cikin jirgin a lokacin da ya kife, ya kara da cewa yawancin wadanda suka nutse yara ne.

Ya bayyana cewa, 14 daga cikinsu ‘yan kauyen Tsabu ne, hudu kuma ‘yan kauyen Dogon Hawa.

Ya kara da cewa an yi jana’izar 15 daga cikin wadanda suka mutu a yau (Alhamis) a karamar hukumar yayin da wasu shida kuma ba a gansu ba.

Har yanzu ana ci gaba da aikin nema da ceto a cikin kogin.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da rundunar ‘yan sandan ta bayar a lokacin gabatar da rahoton.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci