OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

A Mayar Da Mulkin Shugabancin Kasar Nan Kudu— Dattawan Kudancin Najeriya

A Mayar Da Mulkin Shugabancin Kasar Nan Kudu— Dattawan Kud

Kungiyar shugabannin yankin kudanci da kuma tsakiyar kasar nan ta gudanar da taron neman a mayar da mulki kudu a kakar zaɓen 2023 a Abuja babban birnin ƙasar.

A cikin sanarwar da ta fitar a karshen taron na ranar Alhamis wanda ya samu halartar tsaffin gwamnoni, da ministoci, da ƴan majalisun tarayya da na jihohi, manyan ƴan siyasa da kwararru daga shiyyar Kudu da tsakiyar Najeriyar, kungiyar ta yi kira ga dukkanin jam’iyyun siyasa. su kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudu.

Sashin BBC Hausa ya ruwaito cewa ta kuma yi gargaɗin cewa duk wata jam’iyya da ta gaza yin hakan kada ta yi tsammanin samun goyon bayan shiyyoyin idan zaɓe ya zo.

‘’Tun da ɗan arewa ne ya yi mulki na tsawon shekara 8 to lalla ya kamata shugabanci ya koma Kudu, duk wata jam’iyya da ta ƙi yin haka kuwa za ta gani a kwaryar shanta’’ inji wannan sanarwa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci