OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Babu Sunan Osinbajo Cikin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu

2023: Babu Sunan Osinbajo Cikin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

Shettima and Tinubu

Bayan shafe makwanni ana ta cece-kuce, a ƙarshe ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Tinubu ta ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓe mai wakilai 422 gabannin zaɓen shugaban ƙasa.

Wasu daga cikin waɗanda ke cikin jerin sunayen sun haɗa da Cif Bisi Akande, Cif John Odigie-Oyegun, Cif Olusegun Osoba, Alhaji Tanko Yakasai, Zainab Asipita Ogundana da wasu mutane 69 a matsayin masu yaƙin neman zaɓe.

Jerin sunayen wanda aka fitar da safiyar yau Asabar a rahoton Vanguard ya ƙunshi wasu ƴan takarar shugaban ƙasa da dama da suka yi watsi da su.

Wani abin mamaki shi ne, mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, wanda shi ma ya tsaya takarar jam’iyyar APC, bai shiga cikin jerin sunayen ba, lamarin da ya daɗa tabbatar da matsalar dake tsakaninsa da tsohon ubangidansa na siyasa, Tinubu.

Haka kuma ya ƙunshi gwamnonin jihohi da tsoffin sojoji da wasu mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu.

A cikin jerin sunayen, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai rike mukaminsa na shugaban kwamitin yakin neman zaben;  yayin da Tinubu yake mataimakin shugaba sai kuma Abdullahi Adamu mataimakin shugaba na biyu.

Sanata Kashim Shettima kuma a matsayin mataimakin shugaba yayin da gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong shi ne Darakta Janar.

Sauran su ne;  Kwamared Adams Oshiomhole (Mataimakin Darakta Janar na Ayyuka);  Hadiza Bala Usman (Mataimakiyar Darakta Janar, Gudanarwa);  da Hon. James Faleke a matsayin Sakatare.

Sauran sun haɗa da Sanata Godswill Akpabio (Mataimakin Shugaban, Kudu-maso-Kudu); Uju Kennedy Ohanenye (Mataimakin Shugaba, Kudu maso Gabas);  Gwamna, Abubakar Badaru ( Kodinato Yankin Arewa/Jigawa); Gwamna Dave Umahi (Kodinato na yanki, Kudu/Ebonyi);  Gwamnan Jihar Kuros Riba.

Sauran akwai Farfesa Ben Ayade (Kodinato, Kudu maso Kudu/Ribas);  Gwamna Yahaya Bello (kodinaton Matasa na Ƙasa ) na jihar Kogi; Dokta Nicolas Felix (Mataimakin Shugaban Matasa na Kasa); da, Gwamna Kayode Fayemi (Mai Gudanarwa/Mai Ba da Shawara, Harkokin Waje na Jihar Ekiti).

Yayin da akasarin Gwamnonin Jihohi da ‘Yan takarar Gwamna a Jam’iyyar aka nada su a matsayin kodinetoci na Jihohi a Jihohinsu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci